Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, camarade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bukaci Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, da ya ajiye mukaminsa idan har ba zai iya ci gaba da kasancewa a tafiyar siyasa daya da Gwamna Abba Kabir Yusuf ba.
Waiya yayi wannan kiran ne cikin wani shirin kai tsaye a gidan rediyon Muhasa, yayin da yake amsa tambaya kan rahotan da ke cewa mataimakin gwamnan na ci gaba da kasancewa a tafiyar siyasar Kwankwasiyya karkashin jagorancin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, duk da sabon salon da siyasar jihar ke dauka.
Kwamishinan ya ce bambancin siyasa a matakin kololuwar gwamnati na iya raunana amana da kuma kawo cikas ga tafiyar da mulki, musamman ganin cewa mataimakin gwamnan shi ne kuma Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi.
Ya kara da cewa wasu kwamishinoni da suka ji ba su jin dadin yadda tafiyar siyasar ta koma sun riga sun yi murabus, don haka ya dace irin wannan mataki ya shafi mataimakin gwamnan shima.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t