Kotu Ta Yi Watsi Da Ɗaya Daga Cikin Kararrakin Da Aka Shigar Kan Nasarar Tinubu

Alfijr ta rawaito Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa da ke Abuja a ranar Litinin ta yi watsi da daya daga cikin kararraki biyar da ke kalubalantar nasarar Bola Tinubu a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kwamitin alkalai biyar na kotun karkashin jagorancin Haruna Tsammani ya yi watsi da karar bayan lauyan mai shigar da kara ya sanar da janye karar.

Wannan dai shi ne kara na farko a cikin kararraki biyar da kotun ta samu da za a saurare shi.

Tun farko dai kotu ta tabbatar wa duk masu shigar da kara cewa za ta yi adalci ga dukkan bangarori.

Lauyoyin, kuma a jawaban su sun tabbatar wa kotu cewa lallai za su bada haɗin kai matuka.

Ƙara ta farko wacce a ka yi watsi da ita ita ce wadda jam’t AA ta kalubalanci nasarar Tinubu bisa dalilin wai ba a saka sunan ɗan takaran ta na shugaban kasa a manhajar iReV ba.

Bayan ƴar taƙaddama da aka samu tsakanin lauyoyi a farkon zaman, A karshe lauyoyi masu kare AA da kansu suka janye karar inda daga bisani kuma kotu ta yi watsi da shi kwatakwata.

Lauyoyi masu kare hukumar zaɓe INEC da na zaɓaɓɓen shugaban kasa Bola Tinubu duk sun amince da hukuncin kotun.

Daily Trust

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *