Kotun sauraren kararrakin zabe tayi watsi da Karar dake Kalubalantar Nasarar Zaben Abdulmumini Jibrin

Kotun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar Tarayya da ke zamanta a Kano a ranar Laraba ta yanke hukuncin cewa Muhammad Saidu Kiru na jam’iyyar APC ya kasa gabatar da shedu masu inganci da za su tabbatar da cewa an tauye hakkinsu a yayin gudanar da ayyukan majalisar wakilai ta Kiru/Bebeji.

An yi watsi da karar da aka shigar kan nasarar Abdulmumini Jibrin Kofa na jam’iyyar NNPP ba ta tabbata ba.

Alkalin kotun uku karkashin jagorancin mai shari’a Ngozi Flora, ya bayyana cewa takardun da bangarorin biyu suka gabatar a gaban kotun sun nuna cewa Abdulmumini Jibrin Kofa ya yi murabus daga mukaminsa na babban sakataren hukumar gidaje ta tarayya, kwanaki 30 gabanin gudanar da zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu. 2023 a kan ikirarin mai shigar da kara.

Kotun ta ce mai shigar da kara ya kasa gabatar da da hujjoji dake tabbatar da cewa an tafka kura-kurai a zaben.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *