Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta karɓi wani ƙorafi daga wani mai suna Abdullahi Baban Karatu, namiji mai shekaru 55 daga ƙauyen Kurmin Ado, ta Kariya Ward, a ƙaramar hukumar Ganjuwa, jihar Bauchi, a ranar Alhamis, 3 ga Afrilu, 2025 da misalin karfe 4:30 na yamma,
Ƙorafin ya shafi wani mutumi mai suna Umar Alhaji Sule, ɗan shekara 50, mazaunin ƙauyen Kurmin Ado, wanda ake zargi da yi wa ƴarsa mai shekara 17, lalata a cikin ɗakin aurensu tun cikin watan Nuwamba 2024 a lokuta daban-daban.
Bayan karɓar ƙorafin, rundunar ta tura ƙwararrun jami’an bincike domin gudanar da bincike cikin sirri tare da kama wanda ake zargin.
A yayin bincike, wanda ake zargi ya amsa laifinsa ba tare da tilas ba, yana mai cewa ya sha yi wa ɗiyarsa fyade sau da dama, wanda hakan ya kai ga daukar ciki har na wata uku kamar yadda rahoton likita ya tabbatar.
A lokacin da aka yi wa yarinyar tambaya, ta tabbatar da abin da mahaifinta ya fada, inda ta bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da mahaifiyarta ta tafi garin iyayenta a Burra, ƙaramar hukumar Ningi, kuma mahaifinta ya yi amfani da damar don aikata laifin. Daga baya, bayan dawowar mahaifiyarta, ta lura da sauyi a jikinta wanda ya nuna tana da juna biyu. Bayan tambayarta, sai ta bayyana cewa mahaifinta ne ke da alhakin cikin.
Kwamishinan ƴan sandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, psc(+), mni, ya bayar da umarnin a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.
Rundunar ƴan Sanda na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD