Labari Mai Dadi: Kasar Dubai Ta Cire Dokar Hana Bawa Ƴan Najeriya Bizar Shiga Kasar

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta cire haramcin biza a kan ‘yan Najeriya, kamar fadar shugaban Najeriya ta bayyana.

Alfijir Labarai ta rawaito wata sanarwa daga fadar shugaban ta United Arab Emirates (UAE) ta ɗauki matakin ne bayan ganawar da Shugaba Bola Tinubu ya yi da takwaransa Mohamed bin Zayed Al Nahyan a yau Litinin a birnin Abu Dhabi.

“Hakazalika, wannan yarjejeniyar na nufin kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na Etihad da Emirates za su ci gaba da shiga da fita a Najeriya nan take,” in ji sanarwar da Ajuri Ngelale ya fitar.

Ta ƙara da cewa yarjejeniyar ba ta ƙunshi biyan wani kuɗi ba a nan kusa tsakanin ƙasashen, yana mai nuni da miliyoyin dalolin da gwamnatin Najeriya ta riƙe wa kamfanonin jiragen na kuɗin tikiti.

Kusan shekara ɗaya ke nan da UAE ta dakatar da bai wa matafiya daga Najeriya biza, a rikicin da ya samo asali tun daga lokacin annobar korona.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *