Labari Mai Dadi: Ma’aikatan KEDCO sun janye yajin Aiki bisa sharadi

FB IMG 1769204861242

Ƙungiyoyin ma’aikatan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) sun janye yajin aikin da suka shiga bayan cimma yarjejeniya da shugabancin kamfanin.

Yarjejeniyar ta samu ne a wani zama da aka gudanar ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026, a Ma’aikatar Wutar Lantarki ta Jihar Kano, tsakanin KEDCO da ƙungiyoyin SSAEAC da NUEE.

A cewar yarjejeniyar, KEDCO zai biya bashin albashin kari na wata na 13 na shekarar 2019 da ya kai kimanin naira miliyan 150, tare da alkawarin biyan bashin kari na shekarar 2025 a watan Fabrairu 2026. Haka kuma, an tabbatar da cewa ba za a gallaza wa wani ma’aikaci ba saboda shiga yajin aikin, yayin da aka shirya sake zama domin warware sauran matsaloli.

Yarjejeniyar ta samu sa hannun shugabannin KEDCO, ƙungiyoyin ma’aikata da wakilan gwamnati.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *