Labari Mai Dadi! UAE ta ɗage takunkumin hana biza ga ƴan Nijeriya

B6

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ta cimma yarjejeniya da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, UAE, na baiwa masu fasfo din Najeriya damar samun bizar tafiya kasar daga yau (Litinin).

Alfijir labarai ta ruwaito ministan yada labaran Najeriya Mohammed Idris ne ya sanar da hakan a yau Litinin a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnatin taraiya, biyo bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya na mako- mako.

“Yanzu za a iya ba masu fasfo din Najeriya biza zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa.”

Sanarwar ta zo kimanin shekaru biyu bayan da UAE ta dakatar da bayar da biza ga ƴan Najeriya bayan da aka dauki tsawon lokaci ana takaddamar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.

Hakan kuma na zuwa ne kimanin watanni biyu bayan da kamfanin jiragen sama na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, Emirates Airlines ya sanar da dawo da zirga-zirgar jiragen sama zuwa Najeriya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *