Lafiya! Gwamnatin Kano Ta Garkame Wani Asibiti Mai Zaman Kansa A Jihar

Gwamnatin jihar Kano, ta rufe tare asibitin Kwanar Ganduje dake unguwar Sharada Karamar Hukumar birni.

Alfijir labarai ta ruwaito babban daraktan hukumar kula da cibiyoyin lafiya masu zaman kansu ta jihar Kano Farfesa Salisu Ibrahim ya bayyana hakan.

Farfesa wanda ke zaman kwamitin ladabtarwa na hukumar lafiya ta jihar Kano ya ci gaba da cewa an rufe asibitin ne saboda wasu laifuka.

Ya bayyana cewa kwamitin ya gudanar da bincike tsawon watanni hudu domin tabbatar da korafe-korafen da aka samu a kan asibitin.

Babban daraktan ya jaddada cewa kwamitin ya yi taro da dama kan lamarin bayan ya karbi koke-koke har 11 kan asibitin.

Farfesa Salisu ya yi nuni da cewa, an gayyaci mai asibitin wanda kuma ma’aikaci ne a cibiyar Iman Wali Urology Center Dr. Kabiru da ya bayyana a gaban kwamitin a lokuta da dama.

Ya kara da cewa kwamitin ladabtarwa ya bayar da shawarar rufe asibitin Palace daga jerin asibitocin jihar, saboda wasu laifuka da suka saba wa dokar kafa hukumar kula da asibitoci masu zaman kansu.

“Daga cikin shawarwarin akwai haramtawa Dr Kabir aiki ko aiki a asibitoci masu zaman kansu dake fadin Kano da kuma cire sunan asibitin Palace daga cikin jerin asibitoci masu zaman kansu a jihar”.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *