Ma’aikatan wutar lantarki sun garkame hedikwatar Kedco ta jihar Kano

Screenshot 20231016 152608 com.android.chrome edit 3178516940138

Ma’aikatan wutar lantarki a ranar Litinin sun rufe kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO), bisa zargin gaza cire musu kudaden fansho da suka yi a cikin watanni 72 da suka gabata.

Alfijir Labarai ta rawaito ma’aikatan da ke karkashin kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE) sun sha alwashin ci gaba da rufe kamfanin har sai an tabbatar da biyan kudaden.

Malam Ado Ririwai, Shugaban kungiyar na Arewa maso Yamma, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na NAN cewa ma’aikatan ba za su bari a ci gaba da irin wannan dabi’ar ba.

Riruwai ya zargi KEDCO da cin zarafin shugabannin kungiyar da ke kokarin yin magana a madadin ma’aikatan.

“Wannan aiki na mulkin mallaka ne; haƙƙin ma’aikata ne su yi yaƙi da abin da yake nasu,” inji shi.

Shugaban kungiyar ya kuma zargi kamfanin da kin bai wa ma’aikatan kiwon lafiya na asali “duk da hadurran da ke tattare da ayyukansu”.

Kokarin samun martanin hukumar ya ci tura yayin da duk ma’aikata, ciki har da ma’aikatan gudanarwa, an tilasta musu ficewa daga harabar hedkwatar kamfanin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *