Majalisar Ƙoli ta Musulunci a Najeriya ta yi Allah wadai da goyon bayan da Amurka ke yi wa Isra’ila

FB IMG 1697541828386

Majalisar koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Ƙasa, NSCIA, a karkashin jagorancin shugabanta, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ta bayyana bakin cikinta dangane da barkewar kazamin yaki a kan Falasdinawa da aka yiwa kawanya a Gaza.

Alfijir Labarai ta rawaito majalisar ta bayyana haka ne a jiya Litinin a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Farfesa Salisu Shehu da Yunus Ustaz Usman (SAN); Mataimaki Sakatare da mai baiwa NSCIA din shawara kan harkokin shari’a na kasa.

Sanarwar ta ce, mummunan harin da aka kai yana da ratsa zuciya, kuma munanan hare-haren da aka kai kan fararen hula abin takaici ne, don haka Majalisar bukaci a dakatar da kai farmakin da ake kai wa Gaza cikin gaggawa.

Majalisar ta ce, bai kamata a karya yarjejeniyar zaman lafiya mai ɗorewa, kuma duk da cewa ana son a bi tafarkin zaman lafiya, amma idan ba a yi adalci ba, zai haifar da rikice-rikice a nan gaba.

Ta bayyana rashin jin dadin ta ga yadda Amurka ta fito fili ta nuna goyon bayanta ga Isra’ila duk kuwa da irin ta’asar da take yi da kuma kisan gilla da take yiwa Falasdinawa kusan shekaru tamanin kenan.

Majalisar ta bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta yi kamar yadda ta yi wa mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu da kuma tabbatar da adalci, inda ta nemi gwamnatin Nijeriya da ta fito fili ta tsaya tsayin daka data nuna goyon baya ga wadanda Isira’ila ke zalunta tare da yi wa kisan kiyashi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *