Mummunar Gobara Ta Tashi A Hedikwatar Ƴan Sandan Jihar Kano

Alfijr ta rawaito da yammacin ranar Asabar wata mummunar gobara ta tashi a hedikwatar yan sandan jihar Kano da ke unguwar Bompai.

Gobarar ta tashi ne daga ofishin Provost ta kuma bazu zuwa sashen kudi, da dakin taro, sannu sai kuma ofishin Kakakin hedikwatar,PPRO da kuma ofishin mataimakin kwamishinan yan sanda Admin da sauransu.

Gobarar ta kone duk ofisoshin da ke saman benen shelkwatar, ofishin Kwamishinan ne kawai Allah ya tsare shi.

Kakakin rundunar ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce zasu gudanar da bincike kan Ibtila’in.

Allah ya kiyaye faruwar haka a nan gaba ameen.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *