Mun Rufe Asusun Canjin kudade 300 Dake Makare Da Kuɗin Ƙasashen Waje – In Ji Shugaban EFCC.

FB IMG 1706852279199 300x169

Daga Aminu Bala Madobi

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta EFFC Ola Olukayode ya ce sun yi nasarar gano wani sabon dandalin canjin kuɗin kasashen ƙetare “da ya fi dandalin Binance muni”.

Alfijir Labarai ta rawaito Ola Olukoyede ya bayyana haka ne a ganawarsa da manema labarai.

Shugaban ya ce hakan ya sa suka rufe asusun banki 300 bisa umarnin kotu da ke da alaƙa da dandalin, wanda ya ce sunansa “P to P” – ko kuma peer- peer.

“Abin da muka gano shi ne ɗaya daga cikin waɗannan asusun ya yi kasuwancin kuɗi sama da dala biliyan 50 cikin shekara ɗaya ba tare da bankuna sun sani ba, kuma babu wanda ya sani,” in ji shi.

Shugaban EFCC ya ƙara da cewa sun gano “akwai mutanen da suke aikata ɓarnar da ta fi ta Binance”.

Game da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, Mista Olukoyede ya ce “ba don sun kai zuciya nesa ba da sun yi musayar wuta da jami’an tsaronsa” lokacin da suka je kama shi a Abuja

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *