An fara gasar karatun kur’ani ta kasa karo na 39 a jihar Kebbi, wanda ya samu halartar mahalarta daga dukkan jahohi 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja.
A jawabin bude taron, gwamnan jihar, Nasir Idris, ya nuna jin dadinsa ga mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar da ya zabi jihar Kebbi a matsayin wadda ta dauki nauyin gudanar da wannan gagarumin taro na Musulunci.
Gwamna Idris ya lura cewa abin farin ciki ne ga jihar ta dauki nauyin wannan muhimmin taron bayan shekaru ashirin.
Yayin da yake yabawa wadanda suka shirya taron bisa aikin da suka yi, Gwamna Idris ya kuma yi maraba da mahalarta taron zuwa jihar.
Shehun Borno, Mai Martaba Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi, wanda ya kasance uban taro, ya jaddada mahimmaci da falalar Alkur’ani mai girma.
A jawabinsa, Mataimakin Shugaban Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto, Farfesa. Bashir Garba, wanda ya wakilci wadanda suka shirya taron a karkashin Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci ta Jami’ar Usman Danfodiyo Sokoto, ya bayyana Alkur’ani a matsayin tushen shiriya da albarka ga bil’adama, ya kuma bukaci mahalarta taron da da su yi amfani da wannan dama domin kara kusantar kur’ani da kuma mahaliccinsu.
Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato ce ke shirya gasar duk shekara ta Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci.
RN
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj