Rundunar Ƴan Sanda ta Kama Sufeton da Ya Kashe Wani Matashi Saboda Ya Ƙi Ba shi Cin Hanci

FB IMG 1718359772575

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta ce ta kama wani dan sanda mai suna Insifekta Nura Ahmad, tare da tsare shi, wanda ya kashe wani matashi dan shekara 20 a jihar, mai suna Ahmed Ibrahim saboda ya ƙi ba da cin hanci.

FB IMG 1718359769697
Marigayi

Alfijir labarai ta dan uwan ​​marigayin, Jabir Ibrahim, wanda ya zanta da Sahara Reporters kan lamarin, ya ce an kashe Ahmed ne da tsakar ranar Laraba a yankin Zamare da ke karamar hukumar Yauri.

Da yake mayar da martani ga rahoton, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi SP Nafiu Abubakar, ya ce an kama jami’in da yayi aika-aikar tare da tsare shi a sashin binciken manyan laifuka na jihar (SCID) domin gudanar da bincike mai zurfi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a lokacin da Sufeto Nura ke bakin aiki a kan titin Zamare zuwa Yauri, sai Ahmad ya zo wucewa ta wajen shine farkon abunda ya faru.

PPRO ya ce, “A dalilin haka ne Sifeton ‘yan sandan ya harbe Ahmad Ibrahim a kirjin sa, inda nan take aka garzaya da shi babban asibitin Yauri, domin yi masa magani, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa.

“Saboda wannan mumunar lamarin, an kama sufeto Nura Ahmad, aka tsare shi a sashin binciken manyan laifuka na jihar (SCID), Birnin Kebbi, domin gudanar da bincike mai zurfi, da nufin bankado al’amuran da suka dabaibaye wannan arangama da kuma rashin da’a na Sufeto na ‘yan sanda. .

“Rundunar tana amfani da wannan damar domin miƙa ta’aziyya ga ‘yan uwa da abokan arziki na marigayi Ahmad Ibrahim tare da addu’ar Allah ya gafarta masa ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure rashin da ba za a iya kwatantawa ba.

“Rundunar tana tabbatar wa jama’a cewa za a yi adalci wajen gudanar da bincike kan wannan mugunyar lamarin kuma za a fitar da sakamakonsa nan gaba kadan.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *