Sakon Taya Murnar Shiga Watan Ramadan Daga Bakin Dan Adalan Mubi Alh Musa Jidda

IMG 152059 28226 1772288678630

Alh Musa Jidda Dan Adalan Mudi na taya daukacin al’ummar musulmin Kano da Najeriya tare da Musulmin duniya baki daya bisa albarkar da Allah ya yi mana na kara riskar watan Ramadan watan falala watan albarka.

Dan Adalan Mubi yayi kira ga shugabanni da yan kasuwa da musu hannu da shuni su ji tsohon Allah wajen sauke nauyin da Allah ya dora musu, musamman a wannan watan na Ramadanul kareem.

Ya kara da cewa duk cikin ayyukan Ka na Alkhairi, watakila daya ne zai shigar da Kai Aljanna, yi ƙoƙarin gwada dukkan aikin Alkhairin da Allah ya baka iko, domin yankar fulotin Aljanna tun kana Duniya…

Hakazalika ya kara kira ga Al umma wajen komawa ga Allah, da kuma kara dage da addu’a wajen neman yardarsa da neman saukin wadannan masifu da suka addabi Al ummar kasar nan Musamman rashin tsaro da tsadar rayuwa.

A karshe yayi addu’ar neman sauki da rangwame daga Allah. Da fatan za muyi Azumi karbabbe.

Ramadan Kareem

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *