Shugaban Ƙasar Nijeriya Ya Nada Jaruma Rahama Sadau Mukami

FB IMG 1712271877089

Rahama Sadau za ta yi aiki ciki ne a kwamitin kula da sashen sanya hannun jari a dandalin kirkira na zamani wato Investment in Digital and Creative Enterprise (IDICE).

Alffijir labarai ta rawaito kwamitin dai an dora masa alhakin lalubo hanyoyin da samo masu saka hannun jari ta fuskar kirkira ta zamani domin bunkasa tattalin arzikin Nigeria.

Mataimaki shugaban ƙasa Kashim Shettima shi ne ya jagoranci rantsar da kwamitin tare da bukatar yan kwamitin da su bada gudunnawarsu sosaiwajen ci gaban tattalin arzikin Nigeria ta fuskar kirkirar zamani ta yadda Nigeria zata yi gogayya da sauran takwarorinta na duniya.

A wata sanarwa da Jarumar kannywood Rahama Sadau ta fitar ta bada tabbacin zata yi aiki tukuru domin sauke nauyin da ya rataya a wuyanta da yan kwamitin baki daya.

Fadan Daba: Gwamnatin kano ta Haramta yin fim din dake nuna daba da daudu” Zamu yi aiki tukuru ta hanyar hada hannu da gwamnatin tarayya da masu zuba jari na kasashen waje da hada hannu da bankunan duniya domin inganta tattalin arzikin Nigeria”.

Sadau ta mika sakon godiyarta ga mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima Bisa amincewa da yayi aka sanyata cikin kwamitin domin ta bada tata gudunnawar ta wajen cigaban Kasa.”

Ina mika godiya ga mai girma shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima bisa yadda suka gamsu ina da gudunmawar da zan bayar wajen cigaban tattalin arzikin kasarta musamman ta fannin dana kware wato fannin kirkirar zamani, Ina matukar godiya bisa wannan karamcin”. Rahama Sadau

FB IMG 1712271866827
Rahama Sadau Facebook

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *