Shugaban Hukumar NMDPRA Injiniya Farouk Ahmed Ya Ajiye Aiki

IMG 213951 171225 1766004009040

Shugaban hukumar kula da albarkatun man Fetur NMDPRA Injiniya Farouk Ahmed ya yi murabus daga mukaminsa.

Hakan ya biyo bayan taƙaddama tsakaninsa da Alhaji Aliko Dangote, lamarin da yasa Dangote ya shigar da korafi ga hukumar ICPC, domin binciken Injiniya Farouk Ahmed kan zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Haka kuma, Babban Daraktan Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Sama (NUPRC), Gbenga Komolafe, shima ya yi murabus daga mukaminsa.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya tabbatar da murabus ɗin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya riga ya zaɓi sabbin shugabanni da za su maye gurbinsu.

A cewarsa, Shugaba Tinubu ya rubuta wa Majalisar Dattawa wasika yana neman a gaggauta tantancewa da amincewa da Oritsemeyiwa Amanorisewo Eyesan a matsayin sabon Babban Daraktan NUPRC, da Injiniya Saidu Aliyu Mohammed a matsayin sabon Babban Daraktan NMDPRA.

Onanuga ya bayyana cewa waɗanda aka zaɓa ƙwararru ne da suka dade suna aiki a fannin mai da iskar gas, yana mai nuna kwarin gwiwa cewa za su bayar da ingantaccen shugabanci a bangaren makamashi na ƙasar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *