Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Asabar 09/12/1445AH – 15/06/2024CE

Screenshot 20240317 131846 com.whatsapp.w4b edit 21836918129479

Daga Baba Usman Gama

Kwamishinonin da suka yi aiki tare da tsohon Nasir El-Rufai sun yi watsi da rahoton majalisar dokokin jihar da ya yi zargin cewa kuɗi naira biliyan 423 zun zurare daga asusun jihar ba bisa ƙa’ida ba.

Allah ya yi wa Hajiya Asmau Ladan daga jihar Kaduna rasuwa a Makka.

Mahajjata za su kwashe wunin yau a Dutsen Arafat suna gudanar da addu’o’i, yayin da su kuma waɗanda ba su samu damar zuwa Hajji ba suke gudanar da azumin nafila don neman rabauta da wannan rana.

Dan majalisar wakilai Yusuf Gagdi daga jihar Plateau ya raba raguna 400 da ₦20 million a mazabar sa domin murnar sallah.

Amurka ta ƙaƙaba wa wata ƙungiyar Isra’ilawa masu ra’ayin riƙau takunkumi, saboda harin da takai da ya lalata kayan agajin da ake kai wa Gaza.

Jam’iyyun ANC da DA sun amince da kafa gwamnatin haɗaka a Afirka ta Kudu.

Ana sa ran cewa za a kwashe mako uku ana fama da ƙarancin lantarki a wasu sassa na ƙasar Ghana sanadiyyar raguwar ƙarfin lantarki da ƙasar ke samu daga Najeriya.

An zaɓi Thoko Didiza a matsayin kakakin majalisar Afirka ta Kudu.

Malaman Kwalejojin ilimi a Ghana sun tsunduma yajin aiki.

Shugaban Rasha ya ce dole ne Ukraine ta janye dakarunta daga yankunan da Rasha ta yi iƙirarin ƙwacewa kafin a fara tsagaita wuta, wani ƙuduri da shugaban Ukraine ya kira ”buƙata irin ta Hitler”.

Amurka da Ukraine sun ƙulla yarjejeniyar tsaro ta shekaru 10.

Mali ta sallami kocin tawagar ƙwallon ƙafarta Eric Chelle.

Hukumar ƙwallon ƙafar Najeriya za ta ɗauko koci daga kasar waje.

Euro: Germany ta sami nasara akan Scotland da ci 5:1 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *