Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Asabar 23/03/2024CE – 13/09/1445AH

Screenshot 20240317 131846 com.whatsapp.w4b edit 21836918129479

Daga Baba Usman Gama

Majalisar Wakilai ta bayar da wa’adin mako hudu na tabbatar da an nemo wadanda suka kashe sojojin Najeriya 17 a Jihar Delta.

EFCC ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Benuwai Gabriel Suswam a gaban Kotu kan zargin ya saci Naira biliyan 3.1.

Jami’an tsaro sun kubutar da Almajirai 16 da akayi garkuwa dasu a jihar Sokoto makwanni 2 da suka gabata.

Gwamna Sule na jihar Nasarawa ya umarci a yi bincike kan mutuwar ɗalibai 2 mata na jami’ar jihar da suka mutu a wurin wawar tallafin da gwamnati ta kai makarantar.

Amotekun sun kama mutane 2 da ake zargi masu satar mutane ne a makarantun jihar Osun.

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, ta ce ta dauki kwararan matakan tsaro domin tunkarar masu shirin tada zaune-tsaye yayin bikin al’adar tashe ta bana a jihar.

Gwamnan Kano ya yi umarni a gudanar da bincike kan mutanen da gwamnatinsa ta bai wa kwangilar raba wa al’ummar jihar abinci na Ramadan.

Dubban ’yan Najeriya da ke da niyyar tafiya Umrah a wannan wata na Ramadana babu lallai burinsu ya cika saboda rashin biza daga kasar Saudiyya.

’Yan bindiga sun harbe wani sabon ango yayin harin da suka ƙaddamar a kasuwar Madaka da ke Karamar Hukumar Rafi a Jihar Neja.

Majalisar koli ta addinin Musulunci a Najeriya ta nuna damuwa kan makomar aikin Hajjin bana.

Fitacciyar ƴar TikTok ɗin nan ta jihar Kano, Murja Ibrahim Kunya, ta shigar da ƙarar neman beli a gaban babbar kotun tarayya mai zama a jihar Kano.

Akalla mutane 40 ne aka ruwaito sun mutu, wasu sama da 100 kuma suka jikkata sakamakon wani hari da aka kai a wani gidan rawa kusa da birnin Moscow.

Ana fargabar ‘yan gudun hijirar Rohingya 75 sun mutu a haɗarin kwale-kwale kusa da Indonesia.

Jamhuriyar Nijar ta sake buɗe kan iyakarta da Najeriya a yankunan Diffa da Tahoua da Maradi da Dosso.

Likitoci sun shiga kwana na bakwai da fara yajin aiki a kasar Kenya.

Kociyan Bayer Leverkusen Xabi Alonso zai tafi Bayern Munich maimakon Liverpool idan har zai koma wata kungiya a bazaran nan.

Maiyuwuwa Aston Villa ta sayar da dan wasanta na tsakiya na Ingila Jacob Ramsey, don gudun saba wa dokokin cinikayya na sayen ‘yan wasa.

Sada zumunci: Nigeria ta sami nasara akan Ghana da ci 2:1 a wasan jiya.

Sada zumunci: Columbia ta sami nasara akan Spain da ci 1:0 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *