Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Asabar 23/03/2024CE – 13/09/1445AH

IMG 20240103 WA0021

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamiti wanda zai yanke mafi karancin albashin da ma’aikaci zai dauka.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta tabbatar da dakile wani hari da ‘yan bindiga suka kai kan babbar hanyar Buruku zuwa Kaduna.

Rundunar soji ta ce tana samun nasara a yakin da take da masu ta da ƙayar baya da sauran masu aikata manyan laifuka.

Hedikwatar tsaro ta fitar da sunayen mutum 97 waɗanda take nema ruwa a-jallo kan zarginsu da ayyukan ta’addanci da tsatsauran ra’ayi da kuma barazana ga tsaron ƙasar.

Najeriya ta jajanta wa Rasha kan harin da aka kai wani gidan rawa.

Gwamnan jihar Kano ya nuna bacin ransa kan yadda ake gudanar da aikin shirin raba abincin azumi da ake yi a jihar.

Tsohon Ministan Yada Labarai Lai Mohammed, ya ce labaran karya a shafukan sada zumunta suka kusa kashe masa auren shekara 40 da matarsa.

An ƙaddamar da rabon buhun shinkafa 120,000 da Gidauniyar Ɗangote ta ɗauki nauyi albarkacin watan Ramadan a Kano.

Sojoji sun kashe mayakan ISWAP biyar, sun kuɓutar da mata da yara a Borno.

‘Yan bindiga sunyi garkuwa fasinjoji 10 a yankin Jootar da ke Karamar Hukumar Ukum a Jihar Benuwe.

NDLEA ta lalata sama da tan uku na tabar wiwi a wani dajin Jihar Edo.

Sojoji sun ce sun halaka yan ta’adda 5 sun ceto mata 35 da yara 43 a wani samame da suka kai wasu ƙauyuka da ke Arewa Maso Gabas.

Adadin mutanen da suka mutu a wani hari kan gidan rawa a Rasha sun kai 133, a cewar wani kwamitin bincike a Rasha.

Shugaban Rasha yace sun kama duka maharan da suka kai harin gidan rawa.

An gano wani kabari da gawar ‘yancirani 65 a Libya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *