Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Asabar 24/11/1445AH – 01/06/2024CE

IMG 20240103 WA0021

Daga Baba Usman Gama

An bayar da belin Abba Kyari bayan shafe watanni 27 a tsare.

Tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso ya ɗora alhakin matsalolin yankin Arewa kan rashin adalci d rashin ƙwarewar shugabanni tare da bayyana takaicin yadda ake yaudarar mutane da abin duniya lokacin zaɓe.

Yayin da ake ci gaba da dambarwar sarautar Kano, jami’an tsaro sun ci gaba da gadin sarakunan guda biyu. Yayin da ƴan tauri suka mamaye fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, jami’ai daga Gwamnatin Tarayya kuma ke gadin Aminu Ado Bayero.

Ƙungiyar ma’aikatan ruwa ta ƙasa (MWUN) ta bayyana aniyarta ta shiga yajin aikin da NLC da TUC suka kira a fadin ƙasa.

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja ya ba abokan huldarsa wa’adin awanni 72 su biya kudin wuta ko su kwana a duhu.

Gwamnatin Jigawa ta zuba jarin sama da Naira Biliyan 5 a ayyukan tallafawa manoma.

Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta gargaɗi maniyyatan da ke shirin sauke farali, kan sayar wa takari kayansu da hukumar ta ɗinka musu domin neman kuɗi.

Iska mai haɗe da kura ta taso da tsakar ranar yau Asabar daga bisani aka samu saukar ruwan sama a cikin birnin Kano.

Gwamna Jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ƙara wa ma’aikata albashi mafi ƙaranci daga Naira 40,000 zuwa Naira 70,000.

Gwamnatin jihar Filato za ta samar da na’urori na zamani domin magance matsalar tsaro.

Ali Nuhu ya gabatar da lacca kan fina-finan Najeriya a Faransa.

Jamus za ta bar sansanin sojinta na Nijar a bude bisa yarjejeniyar wucin gadi.

Kenya na bikin cika shekara 61 da samun ‘yancin kai.

Indonesia ta bayyana aniyar tura dakaru da ma’aikatan kiwon lafiya zuwa Gaza.

Shugaban Ukraine Zelensky zai yi jawabi a taron tsaro a Singapore.

Ƙasar Estonia tace wataƙila su ne na gaba idan Rasha ta gama da Ukraine.

Kungiyar Al-Nassr ta sha kashi a hannun Al-Hilal a wasan karshe na cin ‘kofin sarki’ Cristiano Ronaldo ya zube kasa tare da fashewa da kuka har aka fitar da shi daga filin.

Kungiyar Real Madrid ta lashe kofin gasar zakarun turai, bayan da ta lallasa Dortmund da ci 2 0 da nema.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *