Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Lahadi 04/02/2024CE – 24/07/1445AH

IMG 20240103 WA0021

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya aike da ta’aziyyarsa kan rasuwar shugaban Namibiya.

Dakarun Najeriya sun kuɓutar da mutane daga hannun masu garkuwa a Taraba.

Allah ya yi wa tsohon Gwamnan jihar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim rasuwa.

‘Yan bindiga sun sako ɗalibai da malaman jihar Ekiti da suka sace.

Gwamnan Kano Abba K. Yusuf yaje Maiduguri dan ta’aziyar ta’aziyyar rasuwar abokiyar zaman mahaifiyar Kashim Shettima da ta rasu Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

INEC ta dakatar da jami’in zaben Karamar Hukumar Jos ta Arewa, Mista Fred Ogboji, kan bacewar sakamakon zaben cike gurbi da aka gudanar a jihar.

Tsohon Kakakin Majalisar jihar Bauchi, Abubakar Y. Sulaiman, da tsohon mataimkinsa Umaru Dahiru Jamilu PDP sunsake komawa Majalisar jihar bayan nasarar da suka samu a zaben cike gurbi da ya gudana a ranar Asabar.

’Yan takarar Jam’iyyar NNPP a zaben cike gurbin da aka gudanar a Kano sun yi nasara a mazabu biyu daga cikin uku.

Dan takarar Jami’yyar PDP, Adamu Yakubu ya lashe zaɓen cike gurbin dan majalisar Tarayya mai wakiktar mazabar Birninkudu/Buji daga Jihar Jigawa.

An rantsar da Nangolo Mbumba a matsayin sabon shugaban ƙasar Namibiya na 4, bayan rasuwar shugaba Hage Geingob da asubahin yau Lahadi.

‘Yan tawayen Houthi sun yi barzanar kai hare-haren ramuwa.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce an kashe ɗaya daga cikin sojojinta a kudancin Gaza a jiya Asabar.

Jami’ai a kasar Chile sun ce gobarar daji ta halaka mutum aƙalla 51.

Rumbun ajiyar makamai da ke Yimdi a Burkina Faso ya kama da wuta.

EPL: Manchester United ta sami nasara akan West Ham da ci 3:0 a wasan yau.

EPL: Wolverhampton ta sami nasara akan Chelsea da ci 4:2 a wasan yau.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *