Takaitattun Labaran duniya na Yammacin Lahadi 29/10/2023 – 14/04/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya mika ta’aziyyar sa ga iyalai, ƴan uwa da gwamnatin Kogi bisa rasuwar Ohinoyi na Ebira, wanda ya rasu yau Lahadi.

APC da ƴar takararta a zaben gwamnan jihar Adamawa, Sanata Aishatu Ahmed (Binani) sun sha alwashin ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun zaɓe ta yanke.

Jami’an ƴan sanda sun ceto wasu mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Dandume da ke jihar Katsina.

Kamfanin NNPC ya ba da tabbacin cewa zuwa karshen shekarar 2024 za a kammala aikin bututun iskar gas da ya tashi daga Ajaokuta-Kaduna-Kano (AKK).

Yan bindiga sun sace hakimin garin Ruwan Rana Magaji Makau a karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara, da wasu mutane 5.

Atiku Abubakar, zai yi wa ’yan Najeriya jawabi da misalin karfe 11:00 na safiyar gobe Litinin.

‘Yan bindiga sun kashe Washima Erukaa da suka yi garkuwa da shi a ranar 23 ga watan Satumba a gidansa da ke Zakibiam ta karamar hukumar Ukum a jihar Benue.

Jirgin ruwa dauke da fasinjoji sama da 100 ya kife a tsakiyar ruwa a Rafin Benue.

Wata mummunar gobara ta ƙone wasu benaye 3 masu hawa 3 tare da lalata kadarori na miliyoyin Naira a wata kasuwa da ke kan titin Dosunmu a yankin tsibirin Legas a jihar Legas.

Hanyoyin sadarwa na waya da internet sun fara dawowa a Zirin Gaza bayan Isra’ila ta katse su yayin da take ƙara kai hare-hare a yankin.

Sojin Isra’ila sunce suna yin bakin ƙoƙarinsu wajen ƙwato mutanen da aka sace.

Shugaban Iran Ebrahim Raisi ya ce ayyukan Isra’ila “sun wuce iyaka” kuma “za su iya tilasta kowa da kowa ya ɗauki mataki”.

An ceto mahaifiyar dan wasan Liverpool Luis Diaz daga hannun masu garkuwa da mutane ranar Asabar amma har yanzu ana neman mahaifinsa a cewar shugaban kasar Colombia Gustavo Petro.

EPL: Manchester City ta sami nasara akan Manchester United da ci 3:0 a wasan yau.

EPL: Liverpool ta sami nasara akan Nottm Forest da ci 3:0 a wasan yau.

EPL: Everton ta sami nasara akan West Ham da ci 1:0 a wasan yau

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *