Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Laraba 07/02/2024 CE – 27/07/1445AH

IMG 20240103 WA0021

Daga Baba Usman Gama

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shattima, ya kaddmar da jiragen yaki don kawar da ta’addnci, a sasanin sojin sama da ke Makurdi Jihar Binuwai.

EFCC ta gayyaci shugabanin jami’o’in Najeriya da ake karbar kudin makaranatar da dala.

Wata babbar kotun tarayya dake zama a Ikoyi, Legas ta umurci gwamnatin tarayya da ta kayyade farashin kayayyaki da man fetur cikin kwanaki bakwai.

Sarkin Zazzau, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli, ya amince da naɗin Alhaji Yusuf Abubakar Hayatu a matsayin sabon Magatakardan Zazzau.

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a Jihar Kano ta dakatar a wani malaminta kan yiwa dalibai gwale-gwale.

Ƴan sanda sun kama waɗanda ake zargin sun shirya zanga-zanga a jihar Neja.

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce talauci da rashin aikin yi da jahilci ne manyan dalilan da ke kara janyo matsalar tsaro a arewacin Najeriya.

Mahara sun kashe sojoji 3 da ‘yan banga 2 a yankin Umaisha da ke Karamar Hukumar Toto a Jihar Nasarawa.

Rundunar ƴan sanda reshen jihar Bauchi, ta gano tarin wasu bindigu da aka boye a ƙarƙashin ƙasa.

Wata kungiya a Jihar Kano ta aike wa majalisar dokokin jihar wasikar neman ta dawo da Sarki Muhammadu Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano, kuma ta rushe sabbin masarautun jihar.

Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce zai rage wa manoma a yankin Damasak kudin fetur domin bunkasa samar da abinci a jihar.

An harba roka kusa da jami’ar Goma a DR Congo.

Yawan wadanda suka mutu a gobarar dajin Chile ya kai mutane 131.

Zaftarewar kasa ta binne motocin bas biyu a Philippines.

AU ta hana Firaministan Nijar shiga zauren taronta a Brazzaville.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *