Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Litinin 11/12/2023 – 27/05/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu na kan hanyar zuwa jihar Borno domin halartar taron shekara shekara na rundunar sojoji.

DSS ta kama babban basarake Cif Obi Nduka Elunor, bisa zarginsa da laifin yin ƙwacen filaye da mallakar bindigogi ba bisa ƙa’ida ba a Asaba jihar Delta.

A wani mataki na kokarin rage farashin gas din girki gwamnatin tarayya ta janye harajin VAT da kudin fito daga gas din girki da ake shigo da shi daga kasashen ketare.

Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya shiga ganawar gaggawa da majalisar zartarwa na jihar.

Sarkin Musulmi yace za su nemi a tabbatar da adalci ga mutanen Tudun Biri.

Ƴan majalisar dokokin jihar Rivers 27 cikin su 32 sun fice daga Jam’iyyar PDP mai mulki a jihar zuwa APC.

Zamfara: An yi kwanaki 2 a jere ana kai hari a Zurmi, an kashe rayuka, wasu suna asibiti da hannun ‘yan bindiga.

Ƴan bindiga sun yi awon gaba da basaraken gargajiya na ƙaramar hukumar Akpabuyo ta jihar Cross Rivers, Etiyin Maurice Edet a gidansa.

Al’ummar Danjibga dake karamar Hukumar Tsafe ta jihar Zamfara na cikin mawuyacin hali sabida ‘yan bindiga.

Gwamnatin Borno ta ƙaddamar da motoci 107 masu amfani da gas da kuma masu amfani da lantarki a wani mataki na rage raɗaɗin janye tallafin man fetur da aka yi a watan Mayu.

’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga da ke yunkurin tare hanya su sace mutane a kan hayan Dutsin-Ma zuwa Kankara a Jihar Katsina.

Sanatan Sokoto ta Kudu, Aminu Waziri Tambuwal ya nada sabbin hadimai guda 64 da za su taimaka masa a harkokin gudanarwa.

Za a binciki masu yaɗa jita-jitar mutuwar mataimakin shugaban Tanzania.

Kashin ƙarshe na sojin Faransa za su fice daga Nijar kafin ƙarshen Disamba.

Ƙungiyar Hamas ta yi gargaɗin cewa babu wani da take garkuwa da shi da zai bar Gaza da ransa har sai an biya buƙatunmu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *