Takaitattun Labaran Na Yammacin Alhamis 14/12/2023 – 30/05/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Hukumar ‘yan sanda ta ce ‘yan ƙasa da damar ɗauar bidiyo da hotunan ‘yan sanda a lokacin da suke bakin aiki.

Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanya hannu kan kasafin kuɗin jihar na shekarar 2024 da ya kimanin naira biliyan 800.

Kwamishinan shari’a na jihar Rivers ya ajiye aiki.

’Yan bindigar da suka sace matan aure da yara a yankin Kubwa da ke Abuja sun sako jaririya da mata biyu daga cikin mutanen.

Gwamnatin jihar Kano ta amince ta biya kudade har naira biliyan 3 kudin diyyar wadanda aka yi wa rusau a jihar.

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce ta halaka mutum 13 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar.

‘Yan tawayen Kamaru sun kaddamar da hari a jihar Cross Rivers a cikin Najeriya.

Kungiyar manyan saktarrin jihar Yobe takarrama Ali Bulama, wani mai haya da Keke-NAPEP da ya tsinci Naira miliyan 9 a babur dinsa, ya mayar wa mai shi

Kotun kasar Wales ta saki matar da aka ɗaure kan laifin kashe ‘ya’yanta huɗu bayan gano kuskuren shari’a.

Shugaban Uganda ya ce sojojin ƙasar sun kashe mayaƙan ƙungiyar ADF kusan 200 a jamhuriyar demokradiyyar Congo, yayin da suke ci gaba da fatattakar mayaƙan.

Wata kotu a Senegal ta ba da umarnin a mayar da sunan tsararren jagoran ƴan hamayya na ƙasar, Ousmane Sonko cikin rajistar zaɓe.

Majalisar dinkin duniya tace yunwa za ta illata kashi 1 bisa 3 na al’ummar Sudan.

Kasar Hungary ta ki amincewa da yunkurin zaman Ukraine mamba a EU.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *