Tarihin Daya Daga Alƙalan Da Zasu Jagoranci Yanke Hukuncin Shari’ar Gwamnan Kano

FB IMG 1704982518594

An haifi mai Shari’a John Inyang Okoro a ranar 7 ga watan yuli na shekara ta 1959 a jihar Akwa Ibom dake kudancin Nigeria.

Ya halarci makarantar firamare ta Methodist school, Nung ukim, daga shekarar 1965 zuwa 1972. Daga nan ya halarci makarantar Boys High School, Oron, daga shekarar 1973 zuwa 1977. Sa’anan ya kuma halacci Makarantar School of Arts & Science daga shekarar 1979 zuwa 1981.

Mai Shari’a John Okoro ya yi karantunsa na jami’a a University of Lagos, Inda ya karanci aiki lauya daga shekarar 1981 zuwa 1984. Daga bisani ya halarci Makaranta koyon aikin lauya, wadda kowanne lauya yake zuwa kafin ya zama cikakken lauya wato School of Low dake jihar lagos, ya kuma zama cikakken lauya a shekarar 1985.

Mai Shari’a John Okoro ya fara aikin shari’a daga matsayin magistrate grade 11 a shekarar 1986, haka yayi ta tafiya har ya zama chief magistrate grade 1 a shekarar 1996.

Ya zama alƙalin babban Kotun jihar Akwa Ibom a shekarar 1998 zuwa 2006. A dai shekarar 2006 ya zama alƙalin kotun daukaka kara, Inda ya ci gaba da aiki har shekara ta 2013.

Mai Shari’a Okoro ya rike mukai a harkar Shari’a da dama, ya kuma taba zama mamba a kotun saurarar kararrakin zabe ta jihar kano a shekarar 1998, ya kuma taba kasancewa cikin alƙalan kotun sauraren kararrakin zaben gwamna da yan majalisu a jihar Ondo a shekarar 2003. Ya kuma zama na 2 cikin alƙalan kotun sauraren kararrakin zaben gwamna da na yan majalisu a jihar Delta a shekarar 2003.

Ya halarci tarukan karawa juna sani da kwasa-kwasai da dama a ciki da wajen Nigeria.

Kwarewa da gogewar aiki ce tasa aka nada shi cikin alƙalan kotun kolin Nigeria a shekarar 2013, majalisar dattawan Nigeria ta amince da nadin nashi a watan October na shekarar ta 2013, daga bisani kuma tsohon alƙalin alƙalan Nigeria Mai Shari’a Aloma Maryam Mukhtar a ranar 15 ga watan Nuwanba na shekarar 2014 ta rantsar da shi a matsayin alƙalin kotun kolin Nigeria.

Mai Shari’a John Okoro shi ne ya jagoranci Shari’ar Zaɓen shugaban kasa da Atiku Abubakar ya daukaka a kotun kolin bayan zaben da suka gwabza da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a shekarar 2023.

Yanzu kuma shi ne wanda zai jagoranci Shari’ar Zaɓen Gwamnan jihar kano da kotun kolin ta sanya ranar juma’a 12 ga watan janairun shekara ta 2024.

Kadaura 24

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *