Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Kudirin Dokar Shekarun Ritayar Alkalai

Alfijr ta rawaito shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Alhamis ya rattaba hannu kan kudirin dokar da ya maida shekarun ritaya bai daya ga jami’an shari’a.

Kudirin shine tabbatar da daidaito a shekarun ritaya da kuma haƙƙin samun fansho na jami’an shari’a na manyan kotuna da kuma tsawaita shekarun ritaya daga shekaru 65 zuwa shekaru 70.

Kudirin ya fassara jami’in shari’a na manyan kotuna kamar haka:

“Ma’aikacin shari’a da aka nada shi zuwa Kotun Koli, Kotun daukaka kara, Babban Kotun Tarayya, Kotun Masana’antu ta Kasa, Babban Kotun Tarayya Abuja, Babban Kotun Jiha, Babbar kotun Shari’a ta jihar, Kotun daukaka kara na babban birnin tarayya, kotun daukaka kara ta shari’a ta jiha, na iya yin ritaya idan ya cika shekara sittin da biyar da haihuwa kuma zai ajiye mukaminsa idan ya kai shekara saba’in” da haihuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *