Wani Mummunan Hadari Ya Rutsa Da Motar Magoya Bayan PDP Mutane Da Dama Sun Mutu

Alfijr ta rawaito Wata babbar mota dauke da magoya bayan jam’iyyar PDP sama da 70 ta yi Mummunan hatsari a jihar Filato, inda mutane da dama suka mutu.

Lamarin ya afku ne a ranar Asabar a kauyen Jwak da ke gundumar Panyam a karamar hukumar Mangu ta jihar bayan taron jam’iyyar na shiyyar da aka gudanar a Pankshin.

Wani  jami’in a hukumar kiyaye aukuwar hadurra ta kasa (FRSC) a Filato Mista Peter Longsan,ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya faruwar lamarin a Jos.

Peter, ya tabbatar da cewa zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane bakwai, ya kuma ce har yanzu ina jiran cikakken rahoto daga mutanen mu da suke wajen.

“An kuma shaida mana cewa sama da mutane saba’in ne a cikin motar da ta yi hatsari a Panyam a Mangu a kan hanyarsu ta komawa Jos,” inji shi.

Ya kara da cewa a halin yanzu wadanda suka jikkata na samun kulawa a wani asibiti da ke garin Mangu.

Caleb Mutfwang, dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar a wata sanarwa da ya fitar, ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

Dan takarar ya ce yana ziyartar wadanda abin ya shafa a asibitoci daban-daban domin sanin halin da suke ciki da kuma matakan da ya kamata a dauka.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Best seller Channel
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *