Wani Mummunan Hatsari Yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 3, Wasu 4, Sun Jikkata A Abuja

kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa, an ajiye motoci hudu da hadarin ya rutsa da su a ofishin ‘yan sanda.

Alfijir Labarai ta rawaito wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da wasu mutane a ranar Asabar da ta gabata yayi sanadiyar rasuwar mutane uku a Abuja, yayin da wasu hudu da suka hada da mata biyu da maza biyu suka jikkata, kuma aka garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu, in ji rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Josephine Adeh, a wata sanarwa da ta fitar, ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na dare a Dutse Baupma.

“Bayan samun kiran waya daga wani bawon Allah da ke kusa da Tipper Garage, jami’an da suka sadaukar da kansu sun kai dauki ga wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Kubwa domin samun kulawar gaggawa,” inji ta.

Adeh ta kara da cewa, an ajiye motoci hudu da hadarin ya rutsa da su a ofishin ‘yan sanda.

“Sun hada da wata mota kirar Toyota Camry mai lamba YAB 355 AH, da Toyota Pilot da wata babbar mota kirar Tricycle mai lamba KUJ 571 VE,” inji ta.

A cewarta, wata mota kirar Toyota Jeep mai lamba BWR 468 CD, wacce ake kyautata zaton ta jami’in tsaron farin kaya ne (DSS).

Adeh ta kara da cewa “Direban motar an bayyana sunansa David C.Y Audu, mazauni Ushafa.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *