Wata Sabuwa! Jam’iyyar NNPP Na Barazanar Korar Engr Rabiu Kwankwaso

Kungiyar shugabannin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ta bukaci dan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata, Sanata Rabi’u Kwankwaso ya yi murabus cikin gaggawa ko kuma a dakatar da shi har abada saboda zarginsa da hannu a cikin ayyukan cin hanci da rashawa.

Alfijir Labarai ta rawaito Shuwagabannin jam’iyyar sun nemi a yi masa cikakken bayani game da abin da suka bayyana a matsayin “alaka marar kyau tsakanin Kwankwaso da jam’iyyar APC a lokacin da kuma bayan babban zabe.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar Kwamared Sunday Oginni ya fitar, ya zargi Kwankwaso da laifin kitsa rikicin NNPP a fadin kasar nan, a wani yunkuri na kwace jam’iyyar daga ainihin mai su da kuma wadanda suka kafa jam’iyyar.

Sanarwar ta ce shugabannin jam’iyyar NNPP sun gano cewa Kwankwaso tare da hadin gwiwar kungiyarsa sun yi zargin gyara kundin tsarin mulkin jam’iyyar don taimakawa a yunkurinsu na yin garkuwa da tsarin jam’iyyar.

“Hakazalika, rashin bin ka’idar tsarin mulki na baya-bayan nan da aka ce an rusa shugabannin jihohi bakwai na Ekiti, Enugu, Neja, Kaduna Katsina, Ribas da Zamfara tun daga matakin jiha da kananan hukumomi zuwa unguwanni a lokaci guda abu ne da ba za a amince da shi ba.

Don haka muna ba Shugaban riko na kasa ba bisa ka’ida ba kuma Sakatare Oladipupo Olayoku da ake zargi da cin hanci da rashawa mara misaltuwa da wuce gona da iri da ya yi murabus da kansa ko kuma ya fuskanci abin kunya na dakatarwa.

“Kungiyar shugabannin jam’iyyar New Nigeria People’s Party suna amfani da wannan dandalin domin yin kira ga wanda ya assasa wannan babbar jam’iyya Dr. Boniface Aniebonam ya tashi tsaye wajen ganin ya janye yarjejeniyar fahimtar da Kwankwaso ya yi ya dawo da jam’iyyar mu.

Muna amfani da wannan dama don yin kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu hakuri da addu’a don bullowar sabuwar Najeriyar mu baki daya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *