Wata Zanga-Zanga Ta Barke A Abuja Kan Tsige  Ndume Daga Bulaliyar Majalisa

Screenshot 20240724 173155 Facebook

Daga Aminu Bala Madobi

Al’ummar Borno ta Kudu sun yi zanga-zanga a Abuja kan tsige Sanatansu, Mohammed Ali Ndume, saboda sukan Gwamnatin Tinubu kan matsin rayuwa

Alfijir labarai ta ruwaito al’ummar Borno ta Kudu sun yi dafifi a Abuja suna zanga-zangar adawa da tsige Sanatansu, Mohammed Ali Ndume, a matsayin babban mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa.

An tsige Ndume ne saboda sukar Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bayan wata wasika da shugabannin jam’iyyarsa ta APC ta kasa suka aika wa majalisar.

An kuma sauke shiga ga mukamin mataimakin shugaban kwamitin majalisar dattawa a kan kasafin kudi.

An maye gurbin Ndume da Sanata Tahir Monguno (APC, Borno ta Arewa) a matsayin babban mai tsawatarwa.

Sai dai masu zanga-zangar a karkashin Kungiyar Cigaban Borno ta Kudu da suka kai taru a Unity Fountain da ke Abuja, sun bukaci shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya mayar da Ndume.

Da yake jawabi ga manema labarai, jagoran masu zanga-zangar Mohammed Ibrahim Biu, ya ce Ndume hazikin Sanata ne wanda ya yi wa al’ummarsa hidima tsawon shekaru kuma ba za a iya hukunta shi ba saboda fadin gaskiya.

Ya ce tsige Ndume daga mukamin babban mai tsawatarwa illa ne ga yankin Borno ta Kudu da ma Najeriya gaba daya, yana mai jaddada cewa dole ne a yi adalci.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *