WhatsApp Ya Kirƙiro Fasahar Buɗewa A Wayoyi 4 Da Lamba Ɗaya

Alfijr ta rawaito Shugaban Kamfanin WhatsApp ya bayyana saki wata sabuwar fasaha wadda za ta bai wa mutum damar amfani da lamba ɗaya ya buɗe whatsaApp a kan wayoyi daban-daban a ranar Talata.

Mark Zuckerberg ya ce yanzu za a iya amfani da lamba ɗaya a buɗe WhatsApp kan wayoyi har guda huɗu.

Ya kara da cewa ta yadda za a iya aika saƙo da hoto da bidiyo, kuma zai kasance babu wanda ya isa ya datse shi, (end-to-end encrypted) a kan duka wayoyin.

Idan wayar da lambar WhatsApp ɗin take ta daɗe ba ta aiki, to sauran WhatsApp ɗin duka za su tsaya su daina aiki.

Da wannan sabuwar fasahar, yanzu yadda shiga, da yadda ake fita WhatsApp zai sauya tsari.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *