Yadda Nisabin Zakka Da Sadaki Da Diyyar Rai, Zai Kasance A Shekarar, 1444/45 Ah 2023

Alfijr ta rawaito hukumar Shari ah ta jihar Kano ta wallafa yadda nusabin zakka, sadaki da diyyar rai yake ta bana 1444 Ah 2023, kamar yadda ta saba duk shekara.

      MAFI KARANCIN SADAKI

₦24, 637 shine mafi karanci, amma mutum zai iya bada sama da haka bisa kyautatawarsa.

   Kimar Yanke Hannu A Sata

₦24,637 shi ne kimar da za a yanke hannu a idan mutum yayi sata.

NISABIN ZAKKA ZAI FARA DAGA ₦1,970,968. 00.

Za a kasa wannan kucin gida (40) wanda zai zamanto ₦49,274.2 shi za a bayar

Idan kudin ya haura Nisabi, za a kasa gida Arba’in (40) a bayar da kashi daya (1/40)

Diyyar Rai A MUSULUNCI :
₦98,548,405,00

Wannan kimar nisabin zai iya sauyawa daga lokaci zuwa lokaci,
sakamakon hawa da saukar Dinare

            ALFIJR LABARAI

NISABIN ZAKKAR DABBOBI
RAKUMA

RAKUMA: Daga (5 – 9) Akuya 1

Daga (10 – 14) Awaki 2.

Daga (15 – 19) Awaki 3

Daga (20 – 24) Awaki 4.

Daga (25) abin da yai sama za a fitar daga Rakuma.

              ALFIJR LABARAI

SHANU: Daga (30) za a ba da Maraki

AWAKI/TUMAKI: Daga (40-120) za a ba da
Akuya/Tunkiya. Idan suka kai dari da ashirin da daya sai a ba da biyu har Zuwa dari biyu da daya, sai a ba da uku, daga nan kowace dari za a ba da ɗaya.

NISABIN ZAKKAR AMFANIN GONA

Abin da ya kai kwano (300) wanda yake daidai da wusiki 5, za a fitar da kashi daya bisa goma (1/10) na noman ruwan sama, kwano (30).

Abin da ya kai kwano (300) wanda yake daidai da wusiki 5, za a fitar da kashi daya bisa ashirin (1/20) na noman rani, kwano (15).

          ALFIJR LABARAI

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Best seller Channel
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.       @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/I4L1E0rIZp23nVG7Mtt47c

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *