Zanga-zangar Rashin Tsaro Ta Kai Masu Zanga-zanga Kurkuku a Jihar Edo.

IMG 20260113 WA0086

Masu zanga-zanga daga garin Ekpoma na Jihar Edo sun shiga komar hukuma bayan wata kotu ta bayar da umarnin tsare su a gidan gyaran hali da ke Ubiaja.

Jaridar Alfijir Ta Rawaito Cewar Masu zanga-zangar sun fito ne domin nuna damuwarsu kan yadda matsalar rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a yankinsu, lamarin da suka ce ya jefa al’umma cikin fargaba da rashin kwanciyar hankali.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun kama masu zanga-zangar ne yayin da suke gudanar da zanga-zangar lumana, inda suka nemi gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakan gaggawa don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Sai dai daga bisani an gurfanar da su a gaban kotu, wadda ta bayar da umarnin a tsare su domin ci gaba da bincike.

Matakin da aka ɗauka ya haifar da muhawara a tsakanin jama’a, inda wasu ke ganin tsare masu zanga-zangar a matsayin tauye haƙƙin faɗar albarkacin baki, yayin da wasu ke jaddada bukatar bin doka da oda. Lamarin ya ƙara tayar da hankali kan yadda ake tafiyar da al’amuran tsaro da ‘yancin jama’a a Jihar Edo.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *