Ƴan Nijeriya sun kusa dena zuwa ƙasashen waje karatu — In Ji Farfesa Gwarzo

📸Alfijir Labarai

Farfesa Abubakar Adamu Gwarzo ya bayyana kwarin guiwar sa na cewa ƴan Najeriya da dama a nan gaba za su daina tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare domin samun ingantaccen ilimi.

Alfijir Labarai ta rawaito Farfesan wanda ya kafa jami’ar Canada ta Najeriya da ke Abuja ya yi wannan tsokaci a lokacin da ya ziyarci makarantar.

Gwarzo ya yi nuni da cewa, da karuwar jami’o’i masu zaman kansu a fadin kasar, yawancin ‘yan kasar za su gwammace su yi karatu a gida nan da shekaru kamar ashirin.

Ya ce kishin bunkasa ilimi mai inganci ya sa shi ya kafa jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria da Franco-British International University da ke Kaduna.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

“Mun tabbatar da hakan a Kano tare da kafa Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria, tare da ingantattun tsare-tsare, ingantattun malamai da kuma cancanta.

“Duba yawan ingantattun jami’o’i masu zaman kansu, za ku yarda da ni cewa makomar ilimi tana da haske sosai. A cikin shekaru 20, yawancin ‘yan Najeriya ba za su je wasu kasashe don neman ilimi mai inganci ba, a gida za su samu ilimin da suke nema,” in ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *