Ƴan sandan Kaduna sun ce sun ceto mutum 11 daga cikin waɗanda aka ɗauke a hanyar Abuja

 Ƴan sandan Kaduna sun ce sun ceto mutum 11 daga cikin waɗanda aka ɗauke a hanyar Abuja
Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce ta ceto mutum 11 daga cikin matafiyan da ƴan bindiga suka sace a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Lahadi.

BBC ta rawaito Kwamishinan ƴan sandan Kaduna ya ce jami’an ƴan sanda da sojoji sun yi ƙoƙarin korar ƴan bindiga kuma sun yi nasarar kuɓutar da mutum 11.

A ranar Lahadi ne ƴan bindiga suka tare hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suka yi garkuwa da matafiya da dama.

Sun kuma kashe wasu ciki har da wani tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Zamfara Alhaji Sagir Hamidu.

Zuwa yanzu hukumomi ba su bayyana yawan mutanen da aka kashe ba da kuma yawan waɗanda aka sace.

Lamarin ya jefa jama’a musamman direbobi da fasinjoji masu yawan bin hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano cikin fargaba.

Fatan u dai Allah ya kawo mana Karshen wannan rashin tsaron a kasar nan baki daya ameen 

Slide Up
x