Na Hango Wanda Zai Zama Shugaban Kasar Nigeria a 2023. Inji IBB

Na Hango Wanda Zai Zama Shugaban Kasar Nigeria a 2023. Inji IBB

Tsohon shugaban ƙasar Najeriya na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana cewar tuni ya hango wanda zai gaji buzun kujerar shugaba Buhari a kakar zaɓe ta 2023.

Jaridar Daily Independent Hausa 24 ta rawaito Ibrahim Badamasi Babangida IBB ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da akayi da shi a gidan TV  (Arise TV) 

“IBB yace Naga wani matashi da shekarunsa basu wuce 60 ba ya ɗare kujerar shugaban ƙasar Najeriya a 2023.”

kuma wannan matashi ya haɗa duk wata cancanta da nagarta da Najeriya ke buƙata idan har aka bashi damar tsayawa.

IBB ya sake cewa ” Ina shawartar ƴan Najeriya da kada su sake su zaɓi mutumin da ya haura shekaru 60 a matsayin shugaban ƙasa.”

“Halin da Najeriya take ciki a yanzu tana buƙatar jagorancin matashi mai ƙwarewa a fannin tattalin arziki da iya siyasa, wanda yake da abokai a dukkan sassan ƙasar nan, wanda ya iya tafiyar da al’umma.” kamar yadda Labarai 24 ta wallafa, a Cewar IBB

Wa kuka Hango a ranku? 

A hasashen da IBB yayi? 

Slide Up
x

One Reply to “Na Hango Wanda Zai Zama Shugaban Kasar Nigeria a 2023. Inji IBB”

Comments are closed.