Saida aka shekara 15 a Faransa ba tare da an ɗauke wutar lantarki ko daidai da minti 5.
Alfijir Labarai ta rawaito shekarar da ta gabata birnin Paris yayi bikin murnar kasancewa gari mafi haske a duniya.
Kuma kaso 70% na makamashin hasken wutar lantarkin da suke takama dashi daga Uranium ɗin da suke ta ɗiba baji ba gani a Nijar kusan shekaru 60.
Amma abin mamaki yanzu haka abirnin Niamey akwai sababbin unguwanni da wutar lantarki bata kai masu ba.
Kuma wutar ba wai ta Nijar bace saboda kusan kashi 70% na wutar lantarkin Nijar daga Najeriya take zuwa.
An ya kuwa Faransa ta san ya kamata ?
Ina ma dai ace yadda ta haska ƙasarta ita ma Nijar ta haskaka ta hakanan.
Wannan ɗaya ne daga ɗaruruwan dalilan da suka dasa mummunar kiyayyar Faransa cikin zukatan ƴan Nijar.
Shiyasa ba abin mamaki bane idan kunga yan Nijar na lale maraba da duk wanda zai kori Faransawa daga ƙasar.




Nijar Hausa 24
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM
Allah ya shiga tsakanin na gari da mugu