Ƙasashen Musulmi Na Taron Gaggawa Don Ɗaukar Mataki Kan Ƙone Al’qur’ani A Sweden

Kungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya OIC na gudanar da wani taron gaggawa a birnin Jeddah na ƙasar Saudiya domin nazarin matakin bai ɗaya da za a ɗauka kan ƙona Al’qur’ani mai girma da aka yi a ƙasar Sweden a ranar Laraba.

Alfijir Labarai ta rawaito Tattaunawar wadda Saudiyya ta shirya za ta nazarci matakan da suka dace a ɗauka kan abin da ƙungiyar ta kira ”abin Allah wadai” da aka aikata.

Tuni dai ƙungiyar ta yi aAllah wadai kan abin da matashin ɗan asalin ƙasar Iraki da ke gudun hijira a Sweden ya aikata a wajen babban masallacin Stockholm babban birnin ƙasar Sweden ranar Idin Babbar Sallah.

Akasarin ƙasashen musulmi sun gayyaci jakadunsu da ke Sweden domin nuna ɓacin ransu da kuma aike wa da saƙon Allah wadai.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *