Ƙilu Zata Ja Bau: An Gano Yadda Takardar Shaidar Karatun Atiku Ke Ɗauke Da Sunan Sadiq Abubakar

FB IMG 1696527773380

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya fito ya bayyana dalilin da yasa satifiket ɗin sa na jarabawar kammala sakandare (SSCE) ke dauke da suna daban, Sadiq Abubakar, maimakon Atiku Abubakar.

Alfijir Labarai ta rawaito ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ya yi wannan ƙarin haske ta bakin Dele Momodu a shafinsa na X.

Momodu wanda shine Daraktan Sadarwa na Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, ya ce wannan bayanin wani martani ne ga zarge-zargen da ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki suka yi wa shugaban nasa.

Ya yi iƙirarin cewa wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC sun yi tambaya kan sunan ‘Sadiq Abubakar’ a cikin takardar shaidar kammala jarabawar WAEC ta Atiku saɓanin sauran takardun sa.

Momodu, ya ce ya mika tambayoyin ga Atiku, wanda ya bayar da amsar saɓanin da aka samu

FB IMG 1697108813750

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *