Ƙungiyar Ƙwadago A Nijeriya Zata Fara Gangamin Yajin Aiki Ranar Laraba

Ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwana 7 ta sauya tsare-tsaren da suka jefa talakawa cikin halin ƙaƙanikayi.

Alfijir Labarai ta rawaito daga cikin tsare-tsaren da NLC ta nemi gwamnatin shugaba Tinubu ta sauya tunani a kai harda tsadar man fetur na baya-bayan nan wanda ya haura N600 kan kowace Lita.

NLC ayyana cewa idan har FG ta gaza yin abinda ya dace cikin mako ɗaya, zata tsunduma yajin aikin gama gari a faɗin Najeriya ranar 2 ga watan Augusta, 2023.

Ta yi kira ga sauran kawayenta ƙungiyoyin kwadugo da su shirya shiga yajin aiki da kuma gagarumar zanga-zanga a faɗin ƙasar nan.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *