Ƙungiyar ƙwadago ta ba gwamnoni wa’adi kan mafi ƙarancin albashin jahohinsu

Screenshot 20231001 054212 com.facebook.katana edit 38423504856636

Ƙungiyar kwadago ta bai wa gwamnonin jihohi wa’adin mako biyu su fara tattaunawa kan batun biyan ƙarancin albashin N35,000 ga ma’aikata a jihohinsu.

Alfijir Labarai ta ruwaito cewa wannan wa’adin ya yi daidai da sharuddan yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin tarayya, da ƙungiyoyin kwadago ta Najeriya suka sanya wa hannu.

Sassan Jihohin ƙungiyoyin ƙwadagon sun ba da wa’adin makonni biyu inda suka tuntubi gwamnonin da su hanzarta aiwatar da shirin biyan ƙarancin albashin.

A wani labarin kuma, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ƙaddamar da shirin bada tallafin kudi naira tiriliyan 1 da nufin taimakawa gidaje miliyan 15 domin rage raɗaɗin tattalin arzikin da ake samu na cire tallafin man fetur.

A ƙarkashin wannan shirin, kowane magidanci zai karbi Naira 25,000 na tsawon watanni uku, wanda ya kai kusan naira tiriliyan 1.13.

Ministar ma’aikatar jin ƙai, Dr. Betta Edu, ta bayyana cewa kimanin ‘yan Najeriya miliyan 61 ne za su ci gajiyar wannan tallafin kudi.

A baya dai shugabannin ƙungiyar ƙwadago sun cimma matsaya da gwamnatin tarayya a ranar 1 ga watan Oktoba, inda ta tanadi cewa duk ma’aikatan tarayya za su karbi ƙarancin albashin naira 35,000 daga watan Satumba, har sai an kammala sabon mafi karancin albashi na kasa

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *