Ƙungiyar ASSOMEG ta taya Abba Kabir Yusuf murnar samun nasara a kotun ƙoli

FB IMG 1687883795522


Kungiyar kafafen yaɗa labarai ta yanar gizo Association of Online Media Guild, ta taya gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano murnar samun nasara a kotun ƙoli.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta raba wa manema labarai ta hannun shugabanta na riko, Abdullateef Abubakar Jos.

A ranar Juma’a nan ne dai kotun ƙoli ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan Jihar Kano bayan da kotun sauraren ƙararrakin zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka soke nasarar sa.

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnan jihar da ya kiyaye kyakkyawar alaƙar da yake da ita da ’yan jarida na yanar gizo, domin Kano ce ta biyu da ta ke da ɗimbin masu kafafen yada labarai na yanar gizo baya ga jihar Legas.

A ƙarshe ƙungiyar ta buƙaci Gwamnan da ya kara inganta ayyukan more rayuwa domin cigaban jihar Kano.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *