Ƴan Bindiga Sun Kashe Ɗan Takarar Sanata Da Mutane 5 Sa’o’i 48 Kafin Zaɓe

Alfijr ta rawaito ƴan bindiga da ke addabar yankin Kudu maso Gabas sun kashe dan takarar sanata mai wakiltar Enugu ta Gabas, Farfesa Oyibo Chukwu.

Wannan lamari da ke zuwa kusan sa’o’i 48 gabanin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da yammacin Laraba, 22 ga Fabrairu, 2023.

An tattaro cewa an kashe dan takarar Sanata ne tare da wasu biyar a Amaechi Awkunanaw, karamar hukumar Enugu ta Kudu a jihar Enugu.

An kuma ce masu kisan sun kona shi da sauran wadanda suka mutu a cikin motarsa.

Dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour, Chijioke Edeoga, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jam’iyyun siyasa na yi wa ‘ya’yan jam’iyyarsa kisan gilla, wadanda ke ganin barazana ce ga bunkasar jam’iyyar Labour a jihar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *