
Alfijr ta rawaito ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata guda biyu a jami’ar tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya.
Rahotonni sun ce ‘yan fashin ɗauke da muggan makamai, sun sace ɗaliban ne a ɗakunan kwanansu da ke wajen makarantar.
Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar, ta ambato kwamishinan ‘yan sandan Zamfara, CP Kolo Yusuf na tabbatar wa iyayen ɗaliban da kuma hukumar makarantar cewa rundunar tana ƙoƙari don ganin ta kuɓutar da su.
Ta ce ‘yan sanda sun samu rahoton sace ɗaliban a ɗakunan kwanansu da ke a wajen makarantar, kuma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba, ta tura jami’anta zuwa wajen da lamarin ya auku.
Sai dai kafin zuwan jami’an tsaron ‘yan fashin sun tsere da ɗaliban, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Haka kuma sanarwar ta ce kwamishinan ‘yan sandan ya tura ƙarin jami’an tsaro don bin sawun ‘yan fashin da kuma kuɓutar da ɗaliban.
BBC
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇