Alfijr ta rawaito akalla kimanin ‘yan mata uku ne na sakandiren yan mata dake birnin yauri ne suka kubuta bayan tattaunawa da bindigar.
Rahotanni sun ce anjima ana tattaunawa tsakanin iyayen yaran da ‘yan bindigar da suke rike da yaran tsawon lokaci.

“An kwashe kwanaki shida ana tattaunawa a dajin kafin a sako mu hudu daga cikin ‘yan matan,” in ji shugaban iyayen kungiyar ‘yan matan makarantar da aka sace a ranar Litinin.
Wadanda aka saki sune Elizabeth Ogechi Nwafor, Esther Sunday da Aliya Abubakar.
Shugaban kungiyar iyayen ‘yan matan makarantar da aka sace, Malam Salim Kaoje ya shaida wa wakilinmu cewa ‘yan matan da aka sako sun isa birnin Kebbi ne a ranar Litinin da yamma.
“Eh sun sako mana uku daga cikin ‘yan matan makarantar ranar Lahadi da yamma. Su na tare damu a hannun Gwamnatin Jihar”, in ji Kaoje.

Sai dai bai bayyana ko an biya wani kudin fansa ba ko ko a’a.
Idan dai za a iya tunawa, an sace dalibai 96 na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri a lokacin da aka kai wa makarantar hari a ranar 17 ga watan Yunin 2021.
Rahotanni sun ce wasu daga cikin ‘yan matan hudu, Bilha Musa, Fa’iza Ahmed, Rahma Abdullahi da Hafsa Murtala, an sake su ne ta hannun shugaban ‘yan bindiga, Dogo Gide a watan jiya.
Ya ce sun biya wasu kudade da ba a bayyana adadinsu ba domin a sako ‘yan matan hudu bayan sun sayar da kadarorinsu da kuma wani asusun tarawa da ya sa ‘yan Najeriya da dama ke taimaka wa iyayen da kudi.
A watan Janairu, Kaoje ya tabbatar da cewa suna tattaunawa da Dogo Gide bayan sun nemi shiga tsakani ta hannun mahaifiyar ‘yan fashin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ