Ƴan Sandan Jihar Bauchi Da Kano Sun Magantu Kan Zargin Masu Shan Jini

‘Yan sandan Bauchi sun ce babu kamshin gaskiya cikin labarin da ake yadawa cewa masu shan jini sun shiga jihar.

Alfijir Labarai ta rawaito rundunar ‘yan sandan Bauchi da ke Nijeriya ta karyata labaran da ake yadawa cewa wasu mata na shiga gidajen jama’a suna shan jininsu.

Ita ma takwararta ta jihar Kano ta yi magana a kan batun amma ta ce tana gudanar da bincike.

A tattaunawarsa da TRT Afrika, kakakin ‘yan sandan Jihar Bauchi SP Ahmed Mohammed Wakil ya karyata rahotannin da ake yadawa a soshiyal midiya cewa wasu mutum 20 da ake zargi da maita sun shiga Bauchi kuma suna shan jinin jama’a.

Ya bayar da misali da wata mata da bidiyonta ya karade shafukan sada zumunta wadda aka yi zargin tana maita, yana mai cewa ba haka lamarin yake ba.

“Matar mai suna Siddika, mazauniyar Unguwar Shekal ce, ta je wata unguwa mai suna Bakin Kura a cikin garin Bauchi domin neman sadaka, sai ta fadi saboda yunwa.

“Sai wasu mata da matasa suka fara jifanta da duwatsu, suna mai cewa mayya ce,” in ji SP Wakil.


Ya bayyana cewa bayan sun samu wannan labarin sai Kwamishinan ‘yan sandan Bauchi CP Auwwal Musa Mohammad ya bayar da umarni aka yi gaggawar ceto matar.

“Binciken da muka yi ya nuna matar tana da tabin-hankali amma ba mayya ba ce, kuma mun mika ta hannun iyalanta,” in ji shi.

SP Wakil ya bukaci jama’a su daina yada jita-jita ko abin da ba su tabbatar da sahihancinsa ba.

Bincike

A Jihar Kano ma, an samu makamancin wannan lamarin inda wani bidiyo ke yawo da ke nuna ana dukan wasu mata kan zargin cewa ‘yan shan jini ne.

Haka ma akwai wasu hotuna da ake yadawa na wata mata wadda aka kama a Karamar Hukumar Gezawa wadda aka yi zargin ta sha jinin matar gidan.

TRT Afrika ta tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, kan wanna batu.

Duk da dai bai tabbatar ko karyata faruwar lamarin ba, ya shaida mana cewa suna gudanar da bincike.

Da muka nemi karin bayani kan ko an kai musu rahotannin faruwar irin wannan batu, sai ya ce “muna gudanar da bincike” kawai.

TRT Afrika

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *