Ɓarayi Sun Sace Kayan Sama Da Naira Miliyan 20 A Matatar Ruwa

Wasu ɓarayi ne sun kai hari a matatar ruwa ta Birninkudu da ke karamar hukumar Birninkudu a jihar Jigawa, inda suka lakaɗa wa ma’aikata duka tare da sace wasu kayayyaki na sama da Naira miliyan 20.

Alfijir Labarai ta rawaito kwamishinan Albarkatun Ruwa, Ibrahim Garba ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci matatar a yau Juma’a.

Garba, wanda ya nuna takaici kan lamarin, ya ce gwamnati za ta dauki tsauraran matakai kan masu yin zagon kasa ga kokarinta na samar da ruwan sha ga al’ummar jihar.

“Wannan abin bakin ciki ne kwarai da gaske. ‘Yan ɓarayi sun sace wasu kayayyaki na sama da Naira miliyan 20.

“Wannan shi ne karo na farko da hakan ke faruwa tun lokacin da aka samar da wannan matatar ruwa a Birninkudu shekaru 50 da suka gabata.

“Hakan na faruwa a fadin jihar kamar yadda ya faru a Kazaure inda aka lalata rijiyoyin burtsatse kusan 20, aka tona wayoyi aka kwashe su, hakanan ya faru a Babura, Gumel da Dutse. Don haka abin yana faruwa sosai,” Garba ya koka.

Daily Nigerian

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *