Ɗalibi ya baiwa tsohon malaminsa kyautar mota da kudin sayen mai na shekara

ALFIJIR 3 1347293163855

Dakta Dominic Nwankwo, tsohon dalibi a makarantar St. John Bosco Seminary, Isuaniocha, karamar hukumar Awka ta Arewa a jihar Anambra, ya mika sabuwar mota ga daya daga cikin malamansa.

Tare da abokan karatunsu, ciki har da shugaban kwamitin amintattu na kungiyar Tsoffin ɗalibai, Mista Valentine Obienyem; shugaba, Comrade Celestine Oguegbu; da kuma babban sakatare, Sir Chidubem Iloghalu, Dokta Nwankwo ya kuma baiwa Monsignor Sylvester Mgbemfulu naira dubu 100,000 duk wata domin sayen man mota tsawon shekara guda.

Alfijir labarai ta rawaito Nwankwo ya kuma baiwa Mgbemfulu Naira dubu N50,000 don gyaran mota nan take da kuma inshorar mota na tsawon shekaru uku.

Da yake gabatar da jawabin a St. Theresa’s Catholic Church, da ke unguwar Nibo a Awka, a jiya Laraba, Dr. Nwankwo ya nuna matukar godiya ga Mgbemfulu bisa koyar da shi da ya yi lokacin yana ɗalibi.

Dokta Nwankwo ya ce: “koyar wa da shawarwari da Mgbemfulu ya bamu sun yi matukar tasiri a rayuwar mu. Ya sadaukar da kai ga ilimi, kuma wannan aikin wata hanya ce ta nuna godiya ta musamman da kuma murnar cika shekaru 50 na limancin coci,” in ji Dokta Nwankwo.

Msgr Mgbemfulu, wanda Francis Cardinal Arinze ya nada shi limamin coci a 1974, ya yi kusan duk tsawon shekarunsa na aiki a makarantun, inda ya kuma koyar da ilmin sinadarai sama da shekaru arba’in.

IMG 20240111 105919
Kyautar Mota

Daily Nigerian

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *